A wannan rana ce ta 17 ga watan Ramadan aka yi yakin Badar-Tarihi

A irin wannan rana ta 17 ga watan Ramadan a shekara ta 2 bayan hijirah a ka yi yakin Badar tsakanin musulmai wanda Manzon A.. (S.A.W) ya jagoranta da kuma kafiran Makkah, inda A… ya baiwa musulmai nasara a wannan yakin, kuma it ace nasara ta farko ga musulmai.

Kuma a wannan ran ace a shekara ta 2 ‘yar Manzon A… (S.A.W) wato Ruqayya matar sayyadina Usmna ta rasu.

Haka zalika a wannan rana ce a shekara ta 40 Sayyadina Aliyu Bn Abi Dalib, ya yi shahada wanda Abdulrahman Bn Muljim ya kashe shi.

A dai irin wannan rana ce ta shekara 85 bayan hijirah Nana Aisha matar Annabi ta rasu aka kuma binneta a makabartar Baqi’ah.

en_USEnglish
en_USEnglish