Mahauta ku fara amfani da sikeli-Shehu Malanta

Shugaban kungiyar mahauta ta jihar Kano, Alhaji Shehu Malanta, ya yi kira ga mahauta da su rungumi dabi’ar nan ta yin amfani da ma’auni wato sikeli a cikin sana’ar su.

Shehu Malanta, ya bayyana hakan ne a ganawarsa da gidan rediyon Dala, ya ce kamata ya yi dukannin mahauta da su fara amfani da sikelin auna nama don zamanantar da sana’ar su.

Ya kuma yi kira ga gwamnati da ta shigo cikin sana’ar don zamanantar da ita duba da yadda sana’ar ake bukatan ta.

en_USEnglish
en_USEnglish