Sai jama’ar gari sun tashi sannan ‘Yansanda za su yi aiki-CP Kano

Sabon kwamishinan ‘yansandan jihar Kano, CP Ahmad Ilyasu, ya ce ‘yansanda kadai ba zasu iya tsare rayuka da dukiyar al’umma ba, don haka akwai bukatar kowa ya bada gudunmawa wajen inganta harkokin tsaro a jihar Kano da kasa baki daya.

CP Ahmad Iliyasu, ya bayyana hakan ne yayin ganawarsa da manema labarai a karo na farko tin fara aikinsa a matsayin kwamishinan ‘yansandan jihar Kano.

Ya kuma ce kudirin sa shi ne tabbatar da kade masu laifi a fadin jihar Kano ta hanyar da doka ta tanadar ba tare da ketare iyaka ko cin zarafin al’umma ba.

Ya kara da cewar, za su bi mai laifi duk inda ya shiga musamman masu kunnen kashi, ya na mai cewa zamani ya wuce da masu aikata laifufuka daban-daban za su sami mafuka a jihar Kano.

Wakilin mu Abba Isah Muhammad, ya rawaito sabon kwamishinan ‘yansandan na kara jan hankali ga al’umma wajen kulawa da harkokin tsaro tare da baiwa rundunar bayanan sirri dan daukar mataki cikin gaggawa.

en_USEnglish
en_USEnglish