Al’umma ku rinka yiwa kasa addu’a -Sunusi II

Maimartaba sarkin Kano Malam Muhammadu Sunusi na II, ya yi kira ga al’umma da su cigaba da yi wa jihar Kano da ma kasa baki daya addu’o’in zaman lafiya.

Malam Muhammadu Sunusi na II, ya yi wannan kiran ne yayin da yake gudanar da addu’ar cikar shekara biyar da rasuwar Alh Ado Bayero, da kuma cikar sa shekara biyar akan karagar mulki, wanda ya gudana a babban masallacin juma’a dake cikin garin Kano.

 

en_USEnglish
en_USEnglish