Amosanin jini ta zama ruwan dare -Dr. Musa K/Na’isa

Wani likita dake Asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano, Dr Musa Kofar Naisa, ya ce cutar amosanin jini cuta ce da ta zama ruwan dare, duba da yadda masu cutar ke karuwa a tsakanin Al’umma, Dr Musa Kofar Na’isa ya bayyana hakanne a ganawarsu da gidan rediyon Dala.

Ya kara da cewa duk mutumin da yaji wani alamu na ciwon gabobi da ya garzaya Asibiti domin ganawa da likita don yi masa gwaji tare da bashi sha warwari.

en_USEnglish
en_USEnglish