Jam’iyyar PDP zata marawa sanata Ali Ndume na APC da sanata Umar Muhammad Bago baya

Bayan wani zama da jam’iyyar ta yi da duk wani mai ruwa da tsaki na jam”iyyar da suka hada da shugabanni,gwamnoni da sanatoci da sauran yan majalisu jamiyyar tace a rikicin da ake na fidda sugabanci a majalisar dattawa sun aminta su marawa sanata Ali Ndumi baya ya zama shugaban majalisar sai kuma sanata

Umar Muhammad Bago ya zama mataimakinsa.

Sanarwar mai dauke da sa hannun sakataren yada labarai na jam’iyyar sanata Umar Tsauri tace ta dau wannan mataki ne domin samar da masalaha a majalisar.

A yau ne dai ake sa ran majalisar zata fidda sabon shugabancin majalisar domin jagorantar zauren majalisar kashi na tara.

jam’iyyar APC dai mai mulkin kasa ta tsayar da matsayarta inda ta yi kira ga ‘yayanta da su marawa sanata Ahmad Lawan baya domin ya zama shugaban majalisar.

en_USEnglish
en_USEnglish