Masu adashin gata su daure su karasa biyan kudaden adashi -Hukumar Alhazan Kano

Hukumar jin-dadin alhazai ta jihar Kano, ta bukaci wadanda suka fara biyan kudin aikin hajjin bana ta tsarin adashin gata, da su cikasa kudadensu don baiwa hukumar damar kammala shirye-shiryen da suka kamata na tafiya kasa mai tsarki.

Mai Magana da yawun hukumar, Hadiza Abbas, ta bayyana haka cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai, ta kuma ce hukumar na sayar da kujerun aikin hajji ne kadai, ta hannun shugabanninta dake kanana hukumomi wato santa ofisas, ko kuma babban ofishinta dake kan titin bamfai.

en_USEnglish
en_USEnglish