Tausayawa marayu na rage musu radadin halin da suke ciki -Arewa Youth Entreprenuer

Kungiyar horars da matasa kan kananan sana’o’in dogaro da kai wato Arewa Youth Enterprenuer ta bayyana cewa tallafawa marayu tare da jansu ajiki na sanya musu farin ciki da walwala da rage musu radadin dake damun su.

Hakan ya fito ne ta bakin shugaban kungiyar Balarabe Uba Abdullahi yayin wata ziyara da kungiyar ta kai gidan marayu domin gudanar da bikin sallah tare, yace akwai bukatar gwamnati da masu hannu da shuni, su ringa ziyartar gidajen marayu akai akai domin ganin irin halin da suke ciki tare da tallafa musu da kayan more rayuwa.

en_USEnglish
en_USEnglish