An gurfanar da wasu mutane 13 a kotu bisa laifin kafa haramtacciyar kungiya a Kano

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta gurfanar da wasu mutane 13 a gaban kotun majistre mai lamba 42 dake Noman saland karkashin mai shari’a Hanif Sunusi, bisa samun su da laifin hada baki da hada haramtaciyar kungiya da mallakar makamai ba bisa ka’ida ba a garin Garu dake Madobi.

Laifukan da su ka sabawa sashi na 97 da 103 da 148 da kuma na 327 tare da na 404 na kundin hukunta masu laifi wanda aka yiwa gyara a shekarar 2014, kunshin zargin dai ya nuna cewa sun hada baki tare da dibar makamai da su ka hadar da gorori da wukake inda suka lalata motar ‘yansanda.

en_USEnglish
en_USEnglish