Ana dab da tashin ‘yan kasuwar dabbobi ta hauran makaranta

Shugaban dattawa na kasuwar dabbobi dake hauran makaranta a karamar hukumar Gwale, Alh Mansur Ashura, ya yi kira ga mahukunta da su kawo masu dauki bisa zargin cewar ana kokarin tashin su daga wurin sana’ar su.

Alh Mansur Ashura, ya yi wannan kiran ne lokacin da yake ganawa da gidan rediyon Dala, ya na mai cewa kamata ya yi a fara sama masu wuri kafin a tashe su da wurin kasuwancin sun a siyar da dabbobi.

en_USEnglish
en_USEnglish