Jarumi Akshay Kumar ya dagawa jarumi Salman Khan kafa

Baban jarumin masana’antar fina finai ta Bollywood dai Akshay Kumar da jaruma Katrina Kaif za su fito a wani fim ne mai suna Sooryavanshi wanda babban Darakta Rohit Shetty ya bayar da umarni.

An kuma zabi ranar Sallah karama ta shekarar 2020 ne domin fitar fim din kasancewar lokacin hutu ne na ma’aikata da ake samun kudi mai yawa idan an sake fim a lokacin.

Sai dai jim kadan da fitar sanarwar da su Akshay kumar suka fitar sai aka ji shima jarumi Salman khan ya bayar da sanarwa cewa zai saki fim dinsa mai suna “Insha Allah” ranar ta Sallah. Fim din da zai fito da jaruma Alia Bhatt wanda kuma babban darakta Sanjay Leela Bhansali zai bayar da umarni

Wannan tasa ake ta samun kace nace ganin cewa dukkansu manyan jarumai ne hakan zai iya sawa ayi asarar dukiya mai yawa la’akari da cewa kowannesu yana kashe kudi mai yawa idan zai yi fim.

Sai dai magoya bayan Salman kan na ganin cewa Salman din shi yake fitar da fim din a duk lokacin bikin Sallah karama.

Ana tsaka da wannan kace nace ne Su Akshay kumar suka sanar da janye fitar fim din nasu Sooryanvanshi daga ranar sallah zuwa ranar 27 ga watan Maris na shekarar 2020 kamar yadda sanarwa ta fito ta shafin twitter na daraktan fim din Rohit Shetty.

en_USEnglish
en_USEnglish