Shugaban kasa Buhari ya sauya sunan filin wasa na Abuja zuwa sunan MKO Abiola

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya sauyawa filin wasa na kasa dake Abuja suna zuwa filin wasa na Mashood Abiyola.

Shugaba Buhari ya sanya sabon sunan ne a lokacin da yake jawabi a kan ranar dimukradiyya yau a Abuja.

Ya kuma ja hankalin ‘yan Nigeria da su rungumi harkar noma da kananan sana’oi don rage talauci,yana mai cewa gwamnatinsa a shirye take ta ci gaba da ingnata bangaren noma kamar yadda ta soma inda sama da kananan manoma miliyan biyu suka ci gajiyar tallafin aikin noma ta cikin tsarin nan na Anchor Grower.

en_USEnglish
en_USEnglish