Yadda za’a magance matsalar sha da ta’ammali da miyagun kwayoyi -Kwamaret Bello Basi

Comrade Bello Basi Fagge

Anyi kira ga mahukunta da al’ummar gari da su hada hannu wajen magance matsalar shan miyagun kwayoyi a tsakankanin al’ummar kasar nan.

wani dan gwagwarmaya, Kwamaret Bello Basi Fagge ne, ya yi wannan kira, ta cikin shirin wannan rayuwa na gidan rediyon Dala a yau, yana mai cewa, za’a magance matsalar sha da ta’ammali da miyagun kwayoyinne kadai, idan gwamnati ta kafa doka mai tsauri akan batun, su kuma iyaye da al’umma suka baiwa gwamnatin hadin kai.

en_USEnglish
en_USEnglish