Yakamata gwamanati ta hade ranar dimokwaradiya data rintsarwa -Hamza Darma

Wani dan siyasa a jihar Kano, kuma daya daga cikin ‘yan kwamatin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na jam’iyar NRC a shekarar 1993, Hamza Usman Darma, ya yi kira ga gwamnati da ta hade rantsuwa da bikin ranar demokradiya ta Nijeriya wuri guda maimakon gudanarwa a ranaku daban-daban kamar yadda aka saba a baya.

Hamza Darma ya furta hakan ne yayin ganawarsa da gidan rediyon Dala, ya kuma bukaci malamai da attajirai da su rinka shiga ana damawa dasu a harkokin siyasa domin samar da cigaban da ya kamata a fadin kasar nan.

en_USEnglish
en_USEnglish