An fara samun cigaba a kotunan Kano bayan tabbatar da babban jojin jiha -Kakakin kotun jiha

Mai Magana da yawun rukunin kotunan jihar Kano, Baba Jibo Ibrahim, ya bayyana cewa an fara samun cigaba a rukunin kotun jihar Kano, sakamakon tabbatar da babban jojin jiha da aka yi a kwanakin baya.

Baba jibo, ya bayyana hakan ne a cikin shirin shari’a a aikace na nan gidan rediyon Dala, a don haka ya kuma yi kira ga ma’aikatan rukunin kotuna da su cigaba da yin aiki tukuru don tabbatuwar cigaban da suka fara gani a wasu daga cikin kotuna.

en_USEnglish
en_USEnglish