An samu cigaba sosai a mulkin dimokradiya -Malam Kabiru Sufi

Wani malami a kwalejin ilimi da share fagen shiga jami’a dake Kano wato CAS, Kabiru Sufi, ya ce shekaru 20 da aka shafe ana gudanar da mulkin demokradiya a fadin kasar nan an sami cigaba bisa daurewar da ta yi a wannan tsawon lokaci.

Kabiru Sufi, ya kuma ce samun demokradiya mai dorewa gagarimar nasara ce da aka samu a fadin kasar nan.

en_USEnglish
en_USEnglish