Anyi kira ga matasa da su hada kai don ciyar da Najeriya gaba -SEDSAC

Shugaban kungiyar bunkasa ilimi da cigaban demokradiya da samar da daidaito a zamantakewa, SEDSAC, Kwamrade Hamisu Umar Kofar Na’isa, ya yi kira ga al’umma musamman ma matasa da su fito su hada kadai don kadai kasar nan ga tudun mun tsira a harkokin siyasa.

Kwamrade Hamisu Umar Kofar Na’isa, ya ce duk kasar da ta cigaba a fadin duniyar nan sai da sa hannun matasa, ya kuma ce suma shugabanni dole ne sai sun rungumi matasa a harkokin siyasa, ba wai kawai su rinka amfani dasu ba a harkokin bangar siyasa.

en_USEnglish
en_USEnglish