Za’a samu cigaba a Najeriya bayan an samu hadin kan kowace kabila -Dr. Sa’id Dukawa

Malami a sashen koyar da kimiyar siyasa a jami’ar Bayero dake Kano, Dr. Sa’idu Ahmad Dukawa, ya ce muddin ana so a ga kasar nan ta samu cigaba dole ne sai an samu hadin kai ga kowace kabila a fadin kasar nan.

Dr. Dukawa, ya bayyana hakan ne yayin zantawarsa da wakilin mu Abubakar Sabo, ya na mai cewa Najeriya kasa ce dunkulalliya duk da dai ‘yan kasar na kokawa dangane da matsalar tattalin arziki.

en_USEnglish
en_USEnglish