Akwai bukatar lauyoyi su dinga taimakawa daurarrun da basu da lauyoyi -DSP. Musbahu Lawal

Mai magana da yawun ma‘aikatan gidajen yari na jhar Kano, DSP. Musbahu Lawan Kofar Nasarawa, yayi kira ga lauyoyi, dasu ringa zuwa gidajen yari, domin taimakawa daurarrun da basu da lauyoyi, musammanma masu manyan laifuka.

Musbahu Lawan Kofar Nassarawa, yayi kiran ne ta cikin shirin shari’a a aikace na nan gidan radiyon Dala, ya ce wajibine su dauki mataki ga duk wanda suka kama, yana ba daidaiba a cikin ma’aikatansu.

en_USEnglish
en_USEnglish