Hisbah ta bukaci maza da su dinga barin kananan ‘ya’yansu a wajen iyaye mata idan an samu rabuwar aure

Mataimakin babban kwamandan hukumar Hisba ta jihar Kano, Malam Idris Ibn Umar, ya yi kira ga mazajen da suka rabu da matayensu da su rika barin kananan yaransu a hannun iyayensu mata, domin samar musu da kulawar data kamata, kamar yadda addinin musulinci ya tanada.

Malam Idris ibn umar ya yi wannan kiranne a ganawarsu da gidan radiyon Dala, yana mai cewa rashin barin kananan yara a hannun iyayen mata da wasu iyayen kanyi, shi ne ke haddasa matsalolin cin zarafin kanan yaran da wasu matan miji suke yi.

en_USEnglish
en_USEnglish