Musulmai su dinga baiwa kalandar musulunci muhimmanci -Mal. Musa Dankwano

Wani malamin addinin musulunci a nan Kano Malam Musa Muhammad Dan-kwano, ya ja hankalin al’ummar musulmai da su rika baiwa kalandar musulunci muhimmanci, maimakon maida hankalinsu akan ta bature kadai.

Malam Musa Muhammad dan kwano ya ja hankalinne da yammacin jiya lokacin da yake tsokaci kan yadda wasu mutane suke wasarairai da sanin watanin musulunci, ta yadda suke gaza sanin sunayen watannin dama jerin lissafinsu.

en_USEnglish
en_USEnglish