NDLEA ta shawarci iyaye mata da su guji jefa kansu cikin ta’ammali da miyagun kwayoyi

Mataimakin shugaban hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi reshen jihar Kano Aliyu Yahaya ya shawarci iyaye mata dasu guji sanya kawunansu cikin halin shan miyagun kwayoyi, wanda yin hakan na barazana ga lafiyarsu.

Aliyu Yahaya ya bada wannan shawarar ne yayin wata bita da aka shiryawa mata tun alokacin azumin watan Ramadan aka kuma karkare ta a jiya litinin a cibiyar Ghuraba dake Nai’bawa yankatako a nan Kano, yana mai cewa shaye-shaye da mata keyi na sanya musu matsaloli da dama da suka shafi lafiyarsu.

en_USEnglish
en_USEnglish