An shawarci malamai da su rinka jan dalibansu a jiki

Shugaban sashen koyar da aikin jarida dake jami’ar Bayero Dr. Haruna Isma’il, ya shawarci malamai musamman ma na jami’o’I, da su rika jan dalibansu a jiki, tare da koyar da su yadda ya kamata ba tare da keta ba, ta yadda zasu rinka fahimtar karatun sosai.

Dr. Haruna Isma’il, ya bayyana hakanne, a yayin taron karrama wani malamin jami’ar dake sashen jaridar, Dr. Ashiru Tukur Inuwa, wannda dalibansa na da da kuma na yanzu suka yi a karshen makon daya bagata sakamakon kammala digiri na uku wato PhD.

en_USEnglish
en_USEnglish