Bamu da shirin hana sana’ar adaidaita sahu -Baffa Babba

Shugaban hukumar Karota, Baffa Babbba dan-Agundi ya karyata rade-radin dake yawo na cewar hukumar zata hana aiki da baburan adaidaita sahu, ko kuma hana su bin wasu bangarori ko kuma titina a jihar kano.

Baffa babba dan-Agundi ya karyata jita-jitanne da safiyar yau, jim kadan bayan kammala shirin shar’a a aikace na nan gidan radiyon Dala, inda a hannu guda kuma ya gargadi jami’an hukumar da su kauracewa yin labe sabo da su kama masu ababan hawa, duba da yadda yin hakan yake haddasa hadura.

en_USEnglish
en_USEnglish