Rashin baiwa kananan hukumomi cin gashin kansu na barazana ga tsaron kasa

Shugaban hadaddiyar kungiyar ma ai‘katan kananan hukumomi ta kasa kwamarade Ibrahim khalil ya bayyana cewa rashin baiwa kananan hukumomi cin gashin kansu abune dake barazana da harkokin tsaro, dama yawaitar samun kudaden haram a tsakankanin al’umma.

Kwamarad Khalil ya bayyana hakanne a ganawarsa da gidan radiyon dala, inda kuma ya kara da cewa duk wani shugaban karamar hukuma da ya biye gwamnansa aka fitar da kudaden al‘umma to su sani cewa hukumar hanacin hanci da rashawa tana kallonsu kuma kungiyarsu bazatai komai akaiba idan aka kamasu.

en_USEnglish
en_USEnglish