An gano iyayen yarinyar da aka tsinci gawarta jiya a Tukuntawa

Karamar yarinyar nan da aka tsinci gawarta da safiyar jiya a wata rijiya dake unguwar tukuntawa, ba tare da sanin iyayenta dama daga inda take ba, a daren jiyan, iyayenta sun bayyana daga unguwar Birget inda suka ce masu garkuwa da mutane ne suka sace ta tun sama da mako guda, suka kuma nemi kudin fansa naira miliyan goma.

Mahaifin yarinyar Alhaji Sani Umar, ya shedawa wakilinmu Aliyu wali, cewa ya biya na ira dubu dari takwas daga cikin kudin, kuma basu bashi yarinyar ba, sai dai kawai ya ji wanan labarin, inda ya fara sheda yarinyar tasa da yarin kunnenta.

en_USEnglish
en_USEnglish