Kotu a Kano ta aike da mutumin da ya kashe matarsa sannan ya binneta zuwa gidan kaso

Babbar kotun jiha mai lamba 8 karkashin mai shari’a Usman Na’abba ta aike da wani mutum gidan kaso, mutumin mai suna Aminu Inuwa wanda ake zarginsa da laifin kashe matarsa ta hanyar yankata da wuka ya kuma binne gawarta a cikin gidansa dake unguwar dorayi.

A zaman kotun na yau lauyan gwamnati Barista Lamido Soron Dinki ya gabatar da shaida daya ya kuma bayyanawa kotun cewa yana da sauran shaidu anan gaba.

en_USEnglish
en_USEnglish