Saurari Shirin Baba Suda Na Jiya Litinin 22/07/2019

Mamakon ruwan da a tabka kamar da bakin kwarya a jiya, ya taho da gawar wani matashi an kuma stinceta a yankin gaida,  zamu ji yadda ko an gano gawar ta ina ce kuma garin yaya,

Itama wata kururrumar rijiya ta ban ruwan kayan lambu gawar wata yarinya aka tsinta a ciki harta kumbura ta fara salubewa,  zamu ji shin ko duk tsawaon kwanakin da tayi a rijiyar, ba’a san tana cikiba su kuma iyayenta suna ina?

Shi kuwa wani mai babaurin adaidaita sahu zarginsa ake yi, ya saka wani tsolon rake jikakke maikaikayi, ya dunga tafkar wata matar aure har sai da mijinta yazo ya kama kwalla, can a gadar karkashhin kasa dake kan titin fanshekara wadda itama take tara ruwan, zamu ji makomar wanan mai bauri.

A banagaren kutu kuwa, wani matashi ne daya saci injin ban ruwan noman kifi, na naira dubu 73 ya siyar  wa da wani dan gwan-gwan naira dubu biyu da dari uku, karshe dan gwa- gwan din ya gudu shi kuma ya samu gurbi a gidan kurkuku, za muji tsawon lokacin da zai kwashe babau zabun tara.

akwai fanin namu naaa,Tabdijan.

DOWNLOAD NOW

en_USEnglish
en_USEnglish