SEDSAC ta bukaci gwamnatin tarayya da ta aiwatar da rugar fulani

Kungiyar bunkasa ilimi da cigaban dimukradiyya tare da samar da daidaito a stakanin al’umma, SEDSAC ta bukaci gwamnatin tarayya da ta zamo mai fada cikawa kan sabon kudirinta na samar da Rigar Fulani, don kaucewa yawaitar rikicin Fulani da makiyaya da ake samu wanda yana daga cikin makasudin fito da tsarin.

Wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar kwamared Umar Hamisu kofar Na’isa, ta rawaito cewa kungiyar ta kuma kalu balanci gwamnatin tarayya kan nuna bangaranci, wajen gudanar da ayyukan raya kasa, tana me cewa kamata ya yi gwamnati ta rungumi dukkanin bangarorin kasar na bakidaya, tare da aiwatar da kudire-kudiren kungiyoyin ci gaban arewacin kasar nan, kamar yadda take faruwa kan kungiyoyin cigaban sauran bagarorin Nigeria.

en_USEnglish
en_USEnglish