Akwai bukatar karin kungiyoyin dalibai a Kano -Idris Muhammad

Mataimakin shugaban kungiyar tsaffin daliban makarantar sakandiren Sharada Tuga, Idris Muhammad ya bukaci daliban da suke gudanar da karatu a halin yanzu, da su rika samar da kungiyoyin dalibai a matakan makarantunsu daban-daban don sadar da zumunta a tsakaninsu da kuma tallafawa makarantun na su.

Malam Idris Muhammada ya yi kiran ne a yayin wani taron kungiyar tsaffin daliban makarantar aji na shekarar 1984, wanda ya gudanan a karshen makon nan, inda yace kungiyoyin tun a matakin karatun, sune suke dorewa har zuwa bayan kammala makarantun.

en_USEnglish
en_USEnglish