Dalibai 12,209 ne suka zana jarrabawar Post UTME a BUK

Dalibai 12,209 ne suka zana jarrabawar Post UTME, a jami’ar Bayero dake nan Kano, domin samun gurbin karatu a jami’ar.

A wata sanarwa da jami’in yada labarai na jami’ar Alhaji Lamara Garba ya rabawa manema labarai a ranar Asabar jim kadan bayan kammala jarrabawar, ya bayyana cewa jarrabawar ta gudana cikin tsari mai kyau kamar yadda aka shirya ta.

en_USEnglish
en_USEnglish