Hukumar Freedom Radio da Dala ta baiwa ma’aikatanta karin horo kan yadda zasu inganta aikinsu

Hukumar rukunin gidajen rediyon Freedom da Dala FM ta gudanar da taron bada horo na musamman ga ma’aikatan gidajen rediyon, a ranakun karshen makon daya gabata.

Taron wanda shugaban tashar Dala FM Ahmad Garzali Yakubu ya jagoranta karkashin tsarin BBC Media Leaders, Ya maida hankali kan muhimman abubuwan da suka shafi kafofin yada labarai, mahalarta taron sun bayyana jin dadi da gamsuwarsu kan wannan horo da suka samu.

en_USEnglish
en_USEnglish