KAROTA tayi gaggawar nema mana makoma -‘Yan Teburan Kantin Kwari

Shugaban kungiyar ‘yan tebura a kasuwar kantin kwari Alhaji Munniru Yunusa Dan-Dago ya yi kira ga hukumar KAROTA data gaggauta samar da makoma ga ‘yan teburan titunan kewayen kasuwar da ta tasa daga wurarensu kamar yadda ta yi musu alkawari.

Dan-dago ya yi kiranne lokacin da yake tsokaci kan makomar ‘yan teburan, yana me cewa, duk da irin kokarin da hukumar ta yi da kuma hadin kan da ‘yan teburan suka bayar don samun nasarar aikin, akawai bukatar samar musu da wasu wuraren don gudun durkushewar kasuwancinsu da kuma lalacewar rayuwar iyalansu.

en_USEnglish
en_USEnglish