Kungiyoyin dalibai su rika tallafawa makarantunsu da kayan karatu -Dagacin Rijiyar Zaki

Dagacin Rijiyar Zaki Alhaji Jibrin Sa’id, ya bukaci kungiyoyin tsoffin dalibai su ringa taimakawa makarantunsu da kayayyakin koyo da koyarwa don bunkasa ilimi a makarantun nasu dama jihar Kano baki daya.

Alhaji Jibril Sai’d ya yi wannan kiranne jim kadan bayan kammala taron kungiyar tsoffin dalibai na makarantar G.S.S. Rijiyar Zaki, wanda ya gudana a karshen makon nan, yana me cewa ilimi wani muhimmin al’amari ne wanda gwamnati kadai ba zata iya masa ba.

en_USEnglish
en_USEnglish