Bada lasisi ga kafafan yada labarai na intanet zai kawo nakasu ga harkar yada labarai

Shugaban sashen nazarin harkokin yada labarai da aikin jarida a tsangayar sadarwa ta jami’ar bayero dake nan Kano dakta Nura Ibrahim, yace yunkurin da gwamnatin tarayya keyi na baiwa gidajen talabijin da rediyo na internet lasisi, zai kawo nakasu ga harkokin yada labarai a kasar nan.

Dakta nura ya kuma ce, in har gwamnati ta dage kan batun, to kamata yayi ta bada lasisi kyauta, ya kuma kara da cewa matukar gwamnati ta sanya kudi domin bada lasisin, babu shakka zai yi sanadiyar kara ta’azzara labarAn bogi a kafar internet.

en_USEnglish
en_USEnglish