Bara da rashin aikinyi baya daga cikin tarihin Hausawa -Farfesa Dangambo

Shehun malamin a fannin hausa farfesa Abdulkadir Dan-Gambo ya ce barace-barace da rashin aikin yi da al’ummar hausawa suka stinci kansu a ciki a yanzu baya daga cikin tarihin al’ummar hausawa.

Farfesa dan gambo ya bayyana hakanne a wani taron hausa na shekara-shekara da kungiyar hauswan Africa ta gudanar a jiya, yana me cewa tarihi ya nuna cewa alummar hausawa mutane masu sana’o’i da kaunar juna sabanin yadda zamani ya lallata wasu daga cikin hausawan a yanzu.

en_USEnglish
en_USEnglish