Dambarwa tsakanin TCN da KEDCO ta haifar da rashin wutar NEPA a Kano

Dambarwa tsakanin hukumomin samar da lantarki da kamfanin dake rarraba wutar lanataki na KEDCO ya haddasa matsanan cin rashin wuta a jihar kano.

Tun a cikin makon jiya ne hukumar TCN tace kamafanin na kedco ya daina daukar wuta, inda shi kuma kamfanin daga baya yace biyan kudin wuta dari bisa dari da hukumar ta bukata shine kalubalen da bazai iya warwarewa ba, a dan haka mafi yawa daga sassan jihar kano suka dau tsahon kwanaki cikin matsalar ta lantarki wadda ya zuwa yau ta fara yin sauki.

en_USEnglish
en_USEnglish