Muna son duk wanda basa samun ruwan sha suyi gaggawar sanar damu Ma’aikatar ruwa ta Kano

Manajan daraktan ma’aikatar samar da ruwan sha injiniya Garba Ahmad kofar Wambai, yayi kira ga al’ummar da basa samun ruwan sha a yankunan su suyi gaggawar sanar da ma’aikatar don kawo musu dauki.

Injiniya Garba ya bayyana hakan yayin zantawarsu da manema labarai, yana mai cewa rashin samun ruwan sha a wasu sassan jihar nan na da nasaba da rashin kawo wa ma’aikatar korafi.

en_USEnglish
en_USEnglish