MUTANEN KANO ZASU FITA DAGA DUHU- inji KEDCO

Sao’i kadan da jinginawa kamfanin rarraba hasken lantarki KEDCO wa’adin kora daga TCN, KEDCO tace yanzu ne alaka ta kara kyautatuwa tsakanin abokan huldar biyu.

Cikin wata sanarwa da shugaban kamfanin na KEDCO Dr. Jamilu Isyaku Gwamna ya aikowa Dala FM da maraicen yau Laraba,yace yanzu haka kamfanin na TCN ya maido da manyan layukan lantarki guda biyu da ya dauke a kwanakin baya, matakin daya jefa jihohin Kano, Katsina Jigawa da kuma jamhuriyar Nijar cikin duhun dukununu

Dr. Gwamna yace wannan ba karamin al’amari ne ga kamfanin KEDCO wajen ganin lantarki ya inganta a jihohi da kamfanin ke hulda dasu.

Shugaban ya mika kokon bara ga kamfanin TCN ya gaggauta

duba matsalar injin raba wutar lantarki mai karfin MVA 150, dake babbar tashar raba wuta dake Dan Agundi, bayan da ya gamu da lalace kwanaki 5 da suka gabata

A karshe kamfanin KEDCO ya mika godiyar sa ga abokan huldar, tare da alwashin samar da yanayi da zai duba bukatu da koken koken al’umma akan ayyukan sa, wanda hakan zai kai ga cimma muradin haskakawa da kawar da duhu a jihohin 3 da kuma jamhuriyar Nijar.

en_USEnglish
en_USEnglish