AN KAMA MIYAGUN KWAYOYI A KANO

Hadakar rundunar tsaro mai yaki da sha da kuma fataucin miyagun kwayoyi ta damke tare da mika muggan kwayoyi a kano.

Shugaban rundunar tsaro na vigilante a kudancin jihar kano Lurwanu Abubakar ne ya jagoranci mika muggan kwayoyin ga shugaban hadakar runduna dake yaki da shan Miyagun kwayoyi Ali Ado Kubau.

Kwayoyin da aka kama sun hadar da Sinadarin Kodin katan 2, Madarar Sukudain galan 10, Sai kwanson Sholisho 100 da kuma Tabar wiwi kilo 1 da rabi.

Shugaban rundunar ta vigilante a kudancin jihar Kano Lurwanu Abubakar yace sun cimma nasarar kame miyagun kwayoyin ne sakamakon bayanai da suke samu daga al’ummar yankin. Wannan ta sanya ya bukaci mazauna birni da kauyukan jihar Kano su shigo a dama dasu dimin dakile muggan ayyuka

A baya bayan nan dai hukumomin tsaro da gwamnatoci na matsa kaimi wajen yaki da dillalan miyagun kwayoyi, bisa yakinin suke haddasa muggan laifuka.

Leave a Reply

en_USEnglish
en_USEnglish