KOTU TA BAIWA HON. ALASAN ADO DOGUWA NASARA

A cigaba da zartas da hukunci kan kararrakin zaben dan majalisar tarayya, kotun sauraron kararrakin zaben karkashin mai sharia Nanye Aganaba ta tabbatarwa Honarabul Alasan Ado Doguwa kujerar sa.Kotun tace masu gabatar da kara basu da cikakkun hujjoji kan zargin magudi da suke yi wa zaben daya tabbatar da nasarar Wakilin Tudunwada da Doguwa a majalisar dokoki ta kasa.Tunda farko dai dan takarar wakilcin Tudunwada da Doguwa ne Air Kwamanda Salisu Yusha’u na jqm iyyar PDP ya garzaya gaban kuliya, yan kalubalantar hukumar zabe ta kasa INEC, jam iyyar APC da Alasan Ado Ado Doguwa, kan sakamakon zaben dan majalisar da aka gudanar a zaben 2019.Sai dai mai shari’ar yayi watsi da dukkanin hujjojin da masu kara suka gabatar, inda yace basu samu cika ta fuskar kamala ba.Wakilin mu Bashir Muhammad Inuwa yace tuni kotun ta kawo karshen zaman ta na wannan rana, bayan data kammala yanke hukunci ka shari’oi dake gabanta a yau Alhamis

Leave a Reply

en_USEnglish
en_USEnglish