ANGA GAWAR WANI LADANI A RATAYE A KANO.

Al’ummar unguwar Medile dake yankin karamar hukumar Kumbotso sun wayi gari cikin alhinin rashin wani matashi da suka gani a rataye.

Dan kamanin shekaru 30 da haihuwa Nasiru Ali Abdussallam ya zarce lokacin da ya saba fitowa da safe, har ta kai aka fara kwankwasa shagon da yake tunda ba’a ganshi a garkame ba, ba kuma a ganshi a bude ba.

Kanin marigayi Nasiru ya shaidawa wakilan dala fm cewar daga bisani ne aa samu nasarar bude shagon da yake ciki inda aka iske shi rataye.

Mallam Badamasi Abdulkadir shine dagacin Shekar Mai Daki yankin dake kulawa da mazabar Medile, ya bayyana matashin a matsayinnzakaran gwajin dafi wajen nman na kai, girmama na gaba da kuma taimakawa iyaye.

Shaidun gani da ido sun tabbatar da cewa Nasiru ya yarda na neman na kai, har ya mallaki shago bayan saana’ar sayar da bulo.

Wata babbar shaida da Nasiru ya samu itace ta ladanci a masallacin unguwar su, koda yake yanayin mutuqar yazo da sarkakiya amma dai kakan sa mai suna Alhaji Ummar Muhd yace ba sa zargin kowa, duk da bbban burin marigayin bai wuce ganin yayi aure ba.

Leave a Reply

en_USEnglish
en_USEnglish