PDP tayi nasara a Shari’ar Dawakin Kudu da Warawa

Kotun sauraron korafin zabe mai mataki na 2 karkashin jagorancin mai shari’a Oyinka Abdullahi ta kori karar da dan takarar majalisar jiha karkashin APC Honarabul Ibrahim Usman ya shigar yana kalubalantar zaben daya baiwa PDP nasara a kakar zabe ta bana.

Zaben na 9 ga watan Maris na shekarar 2019 ya baiwa Honarabul Ibrahim Mu’azzam na jam iyyar PDP nasara kamar yadda hukumar zabe INEC ta ayyana.

Bayan nazarin hujjoji da lawyan APC Barrista Maaruf Muhammad Yakasai ya mikawa kotun cewar anyi magudi, da aringizon kuri’u a wadansu, da baiwa wadanda shekarun su basu kai ba dama, sunyi fatan kotu da zatayi laakari da hujjojin su domin kwace zaben.

Sai dai a karshe kotun ta bayana rashin gamsuwa da wadannan hujjoji na lawan APC inda ta kori karar.

Koda yake lawyan na APC ya shaidawa Bahir Muhammad Inuwa cewar zasu daukaka kara.

Leave a Reply

en_USEnglish
en_USEnglish