Rayuwar wani Jaki ta shiga hadari a Kano.

Wani matashi mai suna Bashir Suraja ya tasamma hallaka wani jaki mallakar makocin sa, biyo bayan takaddama a tsakanin su

Wakilan mu sun shaida mana cewar dama can akwai rashin jituwa tsakanin Bashir da makocin nasu mai suna Mallam mai gidan bulo, da a baya aka taba yi musu sulhu a kotu

Mazauna unguwar Jaen dake yankin karamar hukumar Gwale a birnin Kano sun kara karawa da juna yau juma’a, a karshe rigimar ta juya kan jakin Mallam

Wakilan mu sun ganewa idanun su mummunan rauni da Bashir ya jiwa jakin na Mallam, da har ta kai hanjin cikin sa yana fitowa waje ana kullewa da tsummokara

Rigimar ta bayan nan ta afku ne bayan da cacar baka ta hada matasan biyu yau juma’a, har kowannen su ya koma cikin gida ya fito da makami, amma mutane suka shiga tsakani.

Koda yake al’amarin fa bai yiwa Bashir dadi ba, inda yayi abin nan da bahaushe ke cewa haushin kaza huce kan dami.

Tuni dai ‘yan uwan Mallam suka shigar da maganar gaban hakuma, inda jakin sa ke halin rai kwakwai mutu kwakwai.

Lokacin da wakilan mu suka baro unguwar Ja’en ana jiran isowar tawagar likitoci daga asibitin dabbobi dake unguwar Gwale, domin shiga da Jakin na Mallam tiyata.

Leave a Reply

en_USEnglish
en_USEnglish