Yadda magagin mutuwa ya sa Jaki burma katanga

Labarin jakin nan da wani matashi ya sokawa wuka kusan mun kawo muku shi a makon daya gabata.

Koda yake mummunan yanayi da jakin ke ciki shine babban abinda ya fi tayar da hankali.

Bayan shafe daren juma’a cikin rai kokwai mutu kwakwai, rai yayi halin sa a ranar Asabar da sassafe.

Rahotanni daga unguwar Jaen dake yankin karamar hukumar Gwale a Kano, sun bayyana cewar sai da ta kai jakin ya burma katangar gidan su cikin magagin fitar rai

Wanda ake zargi da aikata laifin ya gurfana gaban kotun majistare dake kan titin gyadi gyadi domin amsa tuhume tuhumen da ake masa

Ana zargin Bashir dan shekaru 23 da laifin kutse cikin gida da kuma haddasa rauni, tuhumar nan take ya amsa ba tare da wahalshe da sharia ba.

Daga nan mai shari’a Auwal Yusuf Usman ya bayar da umarni ga yan sanda su koma da matashin wajensu domin fadada bincike zuwa ranar Talata.

A ranar jum’ar data gabata ne Bashir ya kutsa gidan makocinsu mai suna Mallam, ya farwa kanwar sa mai suna Fatima yar kimanin shekaru 18 da suka da wuka, inda ta samu raunuka a kafada da fuska, da kuma gefen ciki.

Shaidun gani da ido sun ce Bashir ya so yiwa Fatima yankan rago ne inda ya take ta a kasa, amma ta samu taimako daga wata babbar yayar ta inda ta rike wukar, da a karshe itama aka zuge mata hannu.

Ance Bashir ya samu tallafin abokin sa wanda yanzu haka ake nema ruwa a jallo, bayan sun fito daga gidan su Mallam sai suka farwa jakin sa dake kofar gida da sara, inda hanjin sa ya burtso waje.

Wanda safiyar Asabar data gabata jakin ya mutu, bayan shafe tsawon dare cikin numfarfashi sama sama.

Leave a Reply

en_USEnglish
en_USEnglish