Kotu ta bada umarnin sake zabe Kumbotso

Kotun sauraron korrafin zabe ta bada umarnin sake zabe a mazabar Tsamiya dake Mariri a yankin karamar hukumar Kumbotso.

Mai shari’a Nanye Aganaba ya jingine shari’ar zuwa lokacin da INEC za ta cika umarni, tare da umartar Wadanda Ibrahim Umar Balla yake kara wato Mannir Babba Dan Agundi, APC da INEC su biya naira dubu dari 3 ga Balla, a matsayin kudade da ya kashe wajen shigar da kara.

A wani hukuncin kuma kotu mai lamba 3 karkashin mai shari’a Ajoke Adepoju ta kori karar da Ibrahim Jibrin na PDP ya shigar, yana kalubalantar sakamakon zaben majalisar tarayya a karamar hukumar Fagge.

Mai shari’a Adepoju tace zarge zargen da mai korafi ya shiga basu gamsar da kotu ba, hasalima an kaucewa tanadin dokar shigar da kara na shekarar 2010, a sabo da haka kotun ta kori karar.

Leave a Reply

en_USEnglish
en_USEnglish