APC ta kayar da PDP kan kujerar Gaya da Ajingi

Kotun sauraron korafin zabe a kano karkashin mai shari’a Ajoke Adepoju ta kori karar da Usman Mahmud Adamu da jam iyyar PDP suka shigar suna kalubalantar zaben dan majalisar tarayya na yankin karamar hukumar Gaya da Ajingi a zaben daya gabata.

Masu korafin sun kalubalanci Abdullahi Mahmud Gaya, da jam iyyar APC da hukumar zabe ta kasa INEC, cewar zaben yana tattare da magudi, rashawa da kaucewa da dukkanin kaidoji dake cushe cikin dokar zabe na shekarar 2010.

Usman Mahmud  ya gabatar da shaidu guda 6 domin tabbatar da kalubalen daya gabatarwa kotun, koda yake mai shari’a Adepoju tace akwai rashin tsarki a tattare da shaidun  daya gabatar, baya ga gaza tabbatar da hujjoji kan sauran zarge zarge daga bangaren mai

Wakilin mu Bashir Muhammad Inuwa yace a bangaren wadanda ake kara wato Abdullahi Mahmud Gaya, jam iyyar APC da INEC dukkanin su basu gabatar da shaidu ba. A saboda haka mai sharia Ajoke ta kori karar.

Leave a Reply

en_USEnglish
en_USEnglish