Ya rasu yana bautawa dakin Allah

Sunan sa Abul Haq al Halabi, ya rasu yana da shekaru 60 a duniya, sannan ya shafe shekaru 40 yana kiran sallah a masallacin Al Sulaymani dake Jeddah.

Abul Haq dan asalin kasar yankin Sham ne wato Syria, mazaunin kasar Saudiyya daya dora rayuwar sa wajen bautawa masallaci, kuma ya rasu da asubahi yayin da yake karatun alkur’ani.

 

Yana da yaya biyu Khaldoun da Anas, sai kuma yaya mata guda 3, kamar yadda shafin hajj reporters ya wallafa.

 

Leave a Reply

en_USEnglish
en_USEnglish