Kotu ta bayar da Belin Naziru sarkin mawaka

Kotun majistret mai lamba 34 karkashin mai sharia Aminu Usman Fagge, ta fara sauraron wata Shari’a wadda hukumar tace fina finai ta jahar Kano ta gurfanar da Naziru M. Ahmad Wanda aka fi Sani da Naziru sarkin waka.

Tun da farko hukumar ta yi zargin cewar Nazirun ya saki wasu wakoki guda 2 wadanda ba a sahale masa fitar da su ba, wadanda sun hadar da Gidan sarauta da kuma sai Hakuri.

Lokacin da aka karanta masa tuhumar ya ce bai ma San wadannan wakokin ba , daga nan ne lauyan Naziru Barrister Zahraddin Abdullahi ya roki kotun da ta sanya shi a hannun Beli, inda ya yi tawassali da sashi na 35, dana 36 na kundin tsarin mulki kasa.

Koda yake lauyan hukumar Barrister Wada A Wada yayi suka, bisa hujjar idan har  mai shari’a ya bayar da belin sarkin mawakan na sarkin kano zai zamanto babban cikas ga shari’ar. Sai dai lauyan bai kawo hujja daga wani littafin doka ba ko wani misali akan wata shari’a makamancinyar wannan ba, matakin da ya sanya kotun ta bayar da belin sa.

Leave a Reply

en_USEnglish
en_USEnglish