Kungiyar kare hakki na neman wata mata ruwa a jallo

Kungiyar kare hakkin dan adam mai suna Global Community Human Rights ta fidda sanarwar neman wata mata ruwa a jallo, bayan da shirin Baba Suda na ranar talatar data gabata ya kawo wani rahoton cin zarafi, da wata mai hankali ta yiwa wata mai rangwamen hankali.

Rahoton ya kawo halin da mai tabin hankalin ke ciki bayan da wadda ake zargi ta sanya tabarya ta mazge ta, lamarin da ya haifar da sauke kafada har sai da akayi mata daurin karaya.

Shugaban kungiyar ta Global Community Kwamared Karibu Yahaya ya shaida wa Dala fm cikin wata sanarwa cewar al’amarin akwai cin zarafi a ciki, wanda yaci karo da fafutuka da suka sanya gaba wajen tabbatar da yancin kowane dan adam na samun cikakkiyar rayuwa.

Sanarwar tace zasu yi duk mai yiwuwa wajen nemo matar da ake zargi da cin zarafin dan adam domin daukar matakai da suka dace. sanarwa daga nan bata yi karin hasken ko kungiyar zata nufi gaban shari’a da wadda ake zargin ko akasin haka ba, koda yake sautari kungiyoyin kan garzaya gaban shari’ar da nufin nemawa masu karamin karfi yanci.

Leave a Reply

en_USEnglish
en_USEnglish